Babbar kotun jahar Kano, ta yanke wa FrankGeng Quarong hukuncin kisa ta Hanyar rataya har sai ya mutu.
Tun a ranar 16 ga watan satumba 2022, Frank Geng, ya hallaka ummita a Unguwar janbulo dake Kano.
Mai Shari’a Sunusi Ado Ma’aji yanke masa hukuncin ne bayan tabbatar da hujjojin da Masu gabatar da Kara suka yi agaban kotun.