Akwai bukatar Shugaba Tinubu da gwamnoni su kawo daukin gaggawa a karin kudin aikin hajjin 2024 - IHR


Kungiyar sa kai da ke kula da ayyukan hajji da Umrah ta Independent Hajj Reporters IHR ta bukaci gwamnatoci a dukkanin matakai da u sa baki don kawo daukin gaggawa don gudun samun karancin mahajjata a aikin hajjin shekarar 2024.

A daren Lahadin nan dai ne hukumar kula da aikin hajjin Nijeriya ta sanar da karin kudin aikin hajjin shekarar 2024.

A cikin wata sanarwa daga shugaban kungiyar ta IHR Alhaji Ibrahim Muhammad da ya aike wa DCL Hausa ta ce kusan kaso 90% na maniyyatan da suka biya kudinsu 4.9m ba su da ikon biyan karin wasu kudi har 1.9m a cikin kwanaki hudu kacal.

A kan haka ne, kungiyar ke kira da babbar murya ga gwamnoni da gwamnatin tarayya da su shiga cikin lamarin don tallafar tsarin don biyan cikon ga maniyyata a matsayin wani tallafi na musamman.

Sanarwar ta buga misali da cewa ko a jihohi za a dauki lokaci mai tsawo kafin ma sakoneya isa ga maniyyatan da suka biya kudinsu ganin cewa Mafi yawansu manoma ne, sannan hakan na iya daukar wani karin lokaci matsakaici kafin maniyyaci ya iya tara kudin da suka kai N1.9m cikin wannan lokaci.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp