Hukumar da ke kula da Zakka da Wakafi ta jihar Katsina ta sanar cewa ta samu zakkar jimillar kudi Naira milyan 12 daga daidaikun mutane a jihar.
A ta bakin shugaban hukumar Dr Ahmad Musa Filin Samji, hukumar za ta rarraba wadannan kudade ga mabukata da sauran masu karamin karfi a lungu da sako na jihar.
Dr. Ahmad Filin Samji ya ce daga cikin mutanen da da suka ba da wannan Zakka, hada gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda da ya fitar da zakkar kudi ta Naira milyan 10 kuma ya hannanta ta ga hukumar don raba wa mabukata a fadin jihar.
Ya ce da farko Gwamnan bai so a ambaci ya ba da zakkar ba, amma ya nusar da shi cewa Musulunci ya amince a rika sanarwar domin a zaburar da wadanda ba su da niyyar badawa su ji suna so su bayar.
Ya ce hukumar ta yi nasarar dawo da batun hadaya, wato dabbar da ake yankawa idan an kammala aikin hajji a kasar Saudi Arabia da za ta rika kula da shirin don tsaftace ba Alhazai damar kammala aikin hajjinsu yadda ya dace.
Shugaban hukumar ya ce sun gabatar da bukata ga majalisa dokokin jihar Katsina domin ta sa baki a kafa dokar da za ta ba da damar a rika lura da shaidar biyan Zakka ga duk wanda ke neman wani mukami.
Dr Ahmad Musa hukumar da ta fara aiki watanni uku da suka gabata a jihar Katsina, ta yi nasarar kafa ayyukan 'waqafi' masu tarin yawa da zummar amfanar da al'ummar jihar musamman mabukata.
Daga cikin ayyukan akwai gina gidajen marayu 38 da yanzu haka marayu 280 na cikin wadannan gidaje.