Tinubu ya umurci a fito da abinci domin raba wa mazauna Abuja

 Tinubu ya umurci a fito da abinci domin raba wa mazauna Abuja
 Shugaba Bola Tinubu ya umurci Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da ya gaggauta sakin hatsi da kayan abinci ga jama’ar gari, domin dakile illar tabarbarewar tattalin arziki.


 Karamar ministar babban birnin tarayya, Dakta Mariya Mahmoud, ce ta bayyana hakan a ranar Larabar da ta gabata, a wani taron gaggawa da ta yi da masu ruwa da tsaki da shugabannin kananan hukumomi shida na babban birnin tarayya Abuja.


 Ta ce umarnin ya zo ne a wata wasika daga fadar shugaban kasa, ta hannun hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa zuwa ga ministar babban birnin tarayya Abuja, yayin da ta kuma sanar da kafa kwamitin da zai aiwatar da wannan umarni cikin makonni biyu masu zuwa.


 A ranar Lahadin da ta gabata ne wasu mazauna babban birnin tarayya Abuja suka kai hari a wani dakin ajiyar kaya da ke unguwar Gwagwa-Tasha a Abuja, mallakin sakatariyar harkokin noma da raya karkara ta babban birnin tarayya Abuja, inda suka yi awon gaba da kayan abinci tare da lalata ginin.

Post a Comment

Previous Post Next Post