Masara ta yi tsada a Lagos


A dai dai lokacin da Azumin watan Ramadan ke kara gabatowa,kuɗin Buhun Masara ya tashi a kasuwar Mile 12 International Market Legos,inda makon daya gabata aka sayar da Buhun Masarar kan kudi N55,000,sai dai a makon nan, Kudin Buhun Masarar ya kai N65,000, an samu karin kusan Naira dubu 10 kenan. Haka nan kudin Buhun Masarar ya karu a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano, da wancan makon kuɗin buhun ya kama N57,000, yayin da a makon nan kuwa aka sayar da Buhun Masarar N58,000 a kasuwar.

Hakazalika, Masara ta kara tsada a kasuwar Kashere da ke jihar Gombe, a makon da ya shude dai an sayi Buhun Masarar N55,000, yayin da a makon da muke ciki kuwa aka sayar da Masarar N56-57,000.
Idan mu ka yi tattaki zuwa Kasuwar Gombi da ke jihar Adamawa kuwa, Masarar ta yi sauki a wannan makon, sama da makon da ya gabata, an sayi buhun Masarar akan kuɗi N55-57,000, amma an dan samu sassauci N2000 a wannan makon, da aka sayar da buhun N53-55,000.

To ita ma dai kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna Masarar ta fi sauki a wancan makon, an sayi Masarar N55,500, yayin da makon nan kuwa kuɗin buhun ya kama N57,000, wanda hakan ke nuni da cewa an samu karin N1500 cif.

To idan muka je bangaren shinkafar Hausa kuwa ta fi sauki a wancan makon a kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna, inda aka sayi buhun Shinkafar N125,000, sai dai a makon nan ya haure da N5000,Kudin buhun dai, ya kama N130,000 a wannan mai karewa.

A wancan makon dai an sayi shinkafar gida N108,000 a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano, yayin da a wannan makon kuwa shinkafar ta kara N12,000, inda kuɗin buhun ya kama N120,000. Hakan kudin Buhun shinkafar Hausar take a Kasuwar Mile 12 International Market Legos, da aka sayi shi kan kuɗi N120,000, haka nan batun bai sauya tufafi ba a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa, inda a satin nan an sayar da buhun tsabar shinkafar N120,000




A kasuwar Kashere ta jihar Gombe kuwa kuɗin buhun tsabar shinkafar a wannan makon ya kai N115-120,000 hakan akwai na N130,000 a jihar Gomben, sai dai an samu sauƙin N5000 kan kudin na wannan satin da aka sayar da buhun shinkafar har N135,000.

Ita kuwa Shinkafar Bature ta fi sauki a makon nan, a kasuwar Zamani a jihar Adamawa, inda a wancan makon aka sai da shinkafar N82,000, yayin da a makon nan aka sayi buhun shinkafar wajen N75,000

Sai dai a kasuwar Mile 12 International Market Legos kuɗin shinkafar bai sauyi zani ba, a makon da ya shude dai kuɗin N75,000 ne, haka batun ya ke a yanzu ma. 

Shinkafar ta fi sauki a jihohin Kaduna da Gombe, inda a kasuwar Kashere da ke jihar Gombe da aka sayi buhun N80,000, haka nan aka sayar a kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna ma, sai dai an samu tazarar N5000 cif a kasuwar Dawanau na jihar Kano da aka sayar da shinkafar N85,000.

Taliyar Spaghetti ta fi sauki a kasuwar Kashere dake jihar Gombe a wannan makon,inda ake sai da kwalin Taliyar N13,200 ,yayinda a makon daya gabata kuwa aka sayar da kwalin N13,500.

Hakan Spaghetti ta ɗan yi sauki a kasuwar zamani dake jihar Adamawa,an sayi Taliyar N13,500 a wannan makon,amma makon can kuwa Kuɗin kwalin N13,800 ne.

A kasuwar Dawanau na jihar Kano kuwa Taliyar tafi sauki a makon daya shude sama da wanda muke ciki, a wancan N13,500 ne,amma a makon nan ana sayar da kwalin daga 13,500-14,000 dai dai.

A kasuwar Giwa ta jihar Kaduna kuwa N14,500 ne a wannan makon,kudin Taliyar Spaghetti dai bai sauya Tufafi ba a kasuwar Mile 12 International Market Legos,an sayi kwalin kan kudi N14,500
a makon da ya kare,haka kuwa aka sayar a makon nan dake shirin kare wa.

DCL HAUSA A'isha Usman Gebi.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp