Sojoji na neman Bello Turji, Dogo Gide, Ado Aleiro da karin mutane 94 ruwa jallo


Karin wadanda sojojin ke nema ruwa jallo hada Alhaji Shingi, Malindi Yakubu, Halilu Sububu, Dan Bokkolo, Labi Yadi, Kachalla Rugga da Sani Gurgu.

A shekarar 2022 dai rundunar sojojin ta saka sunayen mutane 19, inda ta sanya kyautar Naira milyan 5 ga duk wanda ya ba da bayanan da suka yi jagoranci aka kamo duk mutum daya da ake nema ruwa jallo.

Sai dai a bana, babu tayin irin wannan tukuicin ga wadannan mutane 97 da sojojin ke nema ruwa jallo.

Shiyyar arewa maso yammacin Nijeriya na da mutane 43 da ake nema ruwa jallo, sai shiyyar arewa maso gabas da ke da mutane 33 a yayin da shiyyar kudu maso gabas da arewa ta tsakiya na da mutane 21.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga daraktan yada labaran hedikwatar tsaro ta kasa Maj Gen Edward Buba kamar yadda jaridar PRNigeria ta rawaito.

Post a Comment

Previous Post Next Post