Duk da dai a sanarwar, Gwamnan bai yi bayanin hanyoyin da aka bi aka ceto daliban ba, amma ya ci gaba da godiya har ga mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu da sojoji da daukacin al'ummar Nijeriya da suka yi ta addu'o'in ganin daliban sun kubuta.
A ranar 7 ga wannan wata na Maris ne dai 'yan bindiga suka shiga makarantar firamaren garin Kuriga na karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna suka yi awon-gaba da dalibai kusan 287.