Gwamnatin ta ce tana da zummar kammala aikin gyaran nan da zuwa 29 ga watan Mayu mai zuwa, 2024 kamar yadda jaridar Punch ta rawaito.
Wani babban jami'in gwamnati da ke da hannu dumu-dumu a cikin aikin gyaran, ya tabbatar da cewa aikin ya zamo wajibi duba yadda ambaliyar ruwa ke barazana ga tsohuwar fadar shugaban kasar, inda har wasu wurare sun fara lalacewa.
Hakan na zuwa ne watanni 4 da shugaban kasa Bola Tinubu ya kasafta kashe Naira bilyan 4 don gyaran gidansa da ke Lagos da kuma gidan mataimakin shugaban kasa shi ma a Naira bilyan 3.