Babu dan da na haifa da zan bari ya shiga aikin soja, in ji matar Kanal din soja da aka kashe a Delta

Malama Hawwa Ali, matar marigayi Lt Col Ali A.H ta ce daga cikin ba za ta bar ko da daya ya shiga aikin soja ba.

Malama Hawwa dai ta ce ta yanke wannan shawarar ne biyo bayan kisan gilla da wasu mutane suka yi wa mijinta a kauyen Okuama na jihar Delta.

Matar marigayin ta ce mijinta dai ya rigaya ya ba da rayuwarsa don ci gaban Nijeriya. 

Idan za ku iya tunawa dai, gwamnatin Nijeriya da rundunar sojojin kasar ta samu labarin mutuwar jami'anta 17 a ranar 14 ga watan Maris, 2024 biyo bayan wani kisan gilla da ake zargin al'ummar kauyen Okuama na jihar Delta sun yi musu.

Da jaridar Daily Trust ta tambayi Malama Hawwa ko za ta bar 'ya'yanta su shiga aikin soji, ta kada baki ta ce ba za ta bari wani daga cikinsu ya shiga ba, mahaifinsu dai ya yi, kuma ya ba Nijeriya rayuwarsa.

Ta ce ba za ta iya mantawa da shi a rayuwarta ba, kasancewarsa mutum kamili mai sanin ya kamata da fita hakkin iyalai da iyayensa.

Post a Comment

Previous Post Next Post