Saukar farashin Dala ya sa wasu kayan abinci sun fara sauka a Nijeriya


Farashin kayan abinci na ci gaba da sauka a wasu daga cikin kasuwannin sassan Najeriya, inda a makon nan aka sayi buhun masara ₦52-53 a kasuwar Kashere da ke jihar Gombe.

Idan baku manta dai a makon da ya shuɗe an sayar da buhun masarar ₦58,000 a kasuwar, a wannan makon an samu sauki ko ragowar ₦5,000 kenan.

Ita ma dai kasuwar Mile 12 International Market da ke Lagos, farashin na wannan makon ya sauka, a makon da ya gabata an sayi buhun masara ₦68,000, sai dai a makon nan ₦65,000 ne kudin buhun masara a kasuwar, an samu ragowar Naira 3,000.

Idan muka je kasuwar Dawanau da ke jihar Kano ma an dan samu sassaucin ₦1000 kan farashin makon da ya shude, inda aka sayar da buhun masara ₦58,000 a makon da ya gabata, yayin da makon nan kuwa aka sayi buhun kan kudi ₦57,000 daidai.

Sai dai fa, farashn buhun masarar bai sauya ba a kasuwar Mai'adua jihar Katsina da ke Arewacin kasar Najeriya, inda aka sayar da buhunta kan kudi ₦64,000 a wancan makon, haka nan a wannan makon ma.

To a kasuwar Giwa a jihar Kaduna ma an samu sauƙi kan kuɗin buhun masarar na baya da aka sayi buhun ₦60,000 cif a makon da ya wuce, amma a makon nan kuɗin Buhun ₦57,000 ne, ma iya cewa an samu sauƙin ₦3000 kenan a satin nan da ke shirin karewa a kasuwar Giwa a jihar Kaduna.

A kasuwa Gombi da ke jihar Adamawa kuwa, kuɗin buhun masarar bai canza tufafi ba a wannan makon, an sayi buhun masara kan kuɗi ₦59-60,000, haka kuwa aka saida a makon nan ma.

Shinkafar Hausa ta yi tashin gwauron zabi a kasuwar karamar hukumar Gerie da ke jihar Adamawa. A makon nan, an sayi buhun shinkafar ₦139,000, yayin da a makon da ya gabata kuwa aka sayar ₦127,000, an samu karin N12,000 gabadaya.

Hakazalika, shinkafar Hausar ta ɗan haure a kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna da aka sayar ₦130,000 a 'yan kwanakin nan, amma a makon nan kuma ₦128,000 farashin shinkafar.

A kasuwar Dawanau da ke jihar Kano buhun shinkafa 'yar gida ta sauka a makon da ke dab da ƙarewa, inda aka sayar da buhun shinkafar ₦120,000, amma a satin da ya kare aka sayar ₦130,000, wanda hakan ke nuni da cewa an samu sauƙin ₦10,000 kenan a makon nan.

Sai dai shinkafar ta sauka a kasuwar Mai'adua a jihar Katsina, a wannan makon an sayi buhun shinkafar ₦125,000, saɓanin farashin na baya da aka sayar ₦130,000 daidai.

Ita ma kasuwar Kashere da ke karamar hukumar Akko a jihar Gombe, shinkafa 'yar gida ta fi sauki a makon nan sama da makon da ya wuce, an sayi buhun shinkafar ₦108-110,000, haka nan akwai na ₦115,000, sai dai a makon jiya kuwa ₦115,000 ne -120,000.

Ita kuwa shinkafar bature ta fi sauki a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa, inda aka sayi buhun shinkafar ₦72,000 a makon nan, sai dai a makon da ya gabata aka sayar kan kudi ₦75,000.

Amma shinkafar wajen ta fi tsada a makon nan a kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna da aka sayar ₦78,000 a baya, sai dai a satin nan ₦80,000 ne kuɗin buhun shinkafar.

A kasuwar Dawanau da ke jihar Kano ma dai Farashin shinkafar waje na wannan makon ya sauka, inda aka saida ₦83,000 a satin nan, amma a makon da ya shude ₦87,000 kudin buhun, wanda ake danganta hakan da saukar Dala da a kwanaki ta yi tashin gwauron zabi.

Ita ma dai Jihar Gombe ba a barta a baya ba wajen saukar farashin shinkafar baturen, a makon da ya gabata an sayi buhun shinkafar ₦82-85,000, yayin da a makon nan kuwa aka saya ₦80,000 daidai.

Taliyar Spaghetti dai ta fi tsada a kasuwar Mile 12 International Market da ke Lagos, sama da sauran kasuwannin Arewacin Nijeriya, inda ake sayar da kowane kwalin taliyar ₦15,000 a wannan makon, haka ma a makon da ya gabata.

Har ila yau, taliyar ta fi sauki a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa da a makon nan aka sayi kwalin, N13,200, yayin da a wancan makon aka saida N13,5000 .

Haka nan, a kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna ma ,taliyar ta fi tsada a wancan satin da ake saidawa N15,000, amma yanzu N14,500 ne kuɗin kwalin taliyar a makon nan.

A kasuwannin jihohin Kano da Katsina ma kuɗin kwalin taliyar bai sauya ba, inda ake sayar wa N13,500 a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano, haka kuma aka saya a kasuwar Mai'adua jihar Katsina ma.

Sai dai taliyar ta yi sauki a kasuwar Kashere da ke jihar Gombe, a satin nan ana sayar da kwalin Spaghetti N13,000 daidai, bayan da a makon da ya gabata aka sayar N13,200.

Ga maciya doya kuwa, a wannan makon an sayar da kwaryarta kan kudi Naira 350,000 a kasuwar Mile 12 International Market da ke Ikko.

DCL HAUSA A'isha Usman Gebi.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp