'Yan bindiga sun harbi mutane biyu a Mairuwa jihar Katsina ana tsaka da sallar 'taraweeh'


Wasu mutane dauke da muggan makamai sun kai hari a kauyen Mairuwa na karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina a cikin daren Asabar din nan.

Bayanan da DCL Hausa ta samu sun nuna cewa maharan sun harbi wani fitaccen mutum a garin mai suna Alhaji Lado har hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Majiyar DCL Hausa ta ce maharan da suka zo a kan babura, sun kai samamen ne a masallaci a daidai lokacin da mutane ke sallar 'asham' inda suka harbi Alhaji Lado da karin wani mutum.

Har ya zuwa lokacin hada wannan labarin, babu tabbacin maharan ko sun tafi da wasu mutane ko a'a.

Yanzu haka dai mutanen garin na cikin razani bayan faruwar wannan lamari cikin wannan dare.

Post a Comment

Previous Post Next Post