Daga wakilinmu, Yacouba Maigizawa, Damagaram-Nijar
Kungiyar ECOWAS ta yi Allah wadai da harin da aka kai wa sojojin Nijar da ya sanadiyar rayukan 23 daga cikin su
A cikin wata takarda ce da ta fitar a ranar 23 ga watan nan na Maris, kungiyar ECOWAS ta nuna rashin jin dadin ta da takaici kan harin baya bayan nan a Nijar wanda ya yi awan gaba da rayukan sojojin kasar 23
Kungiyar ta ce tana isar da sakon ta'aziyar ta ga gwamnati da al'amurar kasar Nijar tare da jaddada goyan bayan ta ga 'yan uwan mamatan da sojojin kasar
Kazalika sanarwar ta ce kungiyar na fatan kwanciya ta zama hutu ga wadanda suka kwanta damar tare da fatan manzon sauki ga wadanda suka jikkata
A karshe kungiyar cikin kakkausan kalamai ta ce tana tir da Allah wadai da wannan hari na dabbanci ta kuma tabbatar wa hukumomin na Nijar aniyarta ta bada hadin kai wajen yaki da ta'addanci da kuma tsatsaurar ra'ayi a yankin