Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi kira ga ‘yan kasuwa musamman masu sayar da kayan masarufi da su rage farashin kayan abinci da sauran kayayyaki domin baiwa talakawa damar gudanar da azumin watan Ramadan cikin sauki.
Sarkin ya yi wannan kiran ne a ranar Lahadi a Zariya a lokacin cin abincin rana da aka shirya bayan kaddamar da wani littafi mai suna: “Dauloli a Kasar Hausa” na Farfesa Sa’idu-Mohammed Gusau.
Ado Bayero ya kuma shawarci ’yan Najeriya masu hannu da shuni da su rika taimakawa marasa galihu a lokacin azumin Ramadan..
Ya kuma yi addu’ar Allah subhanahu wata’ala ya nuna mana wannan wata mai alfarma cikin koshin lafiya ya kuma karbi addu’o’in da al’umma zasu gudanar.
Sarkin ya yabawa mawallafin littafin, da ya bayar da cikakkun bayanai kan masarautun Hausawa a Kano, Katsina, Zamfara, Kebbi da Zazzau da dai sauransu.
Ya kara da cewa akwai bukatar kowanne dalibi dake bincike a fannin Ilimin harshen Hausa da tarihinsu ya mallaki littafin littafin don kyautata binciken sa.