Ku kawo rahoton duk wanda ya nema cin hanci a wajenku -Tinubu ya fada wa masu zuba hannun jari

Ku kawo rahoton duk wani Jami'ina da ya nema cin hanci a wajen ku -Tinubu ya gayawa masu zuba hannun jari.




Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya yi kira ga masu zuba jari da su kai rahoton duk wani jami’in Nijeriya da ya nemi cin hanci kafin ya zuba jari a kasar.

Shugaban ya bayyana haka ne a yayin taron kasuwanci da saka hannun jari na Nijeriya da Qatar a birnin Doha a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake tabbatar wa ‘masu zuba jarin kasar Qatar a shirye suke da karfafa alakar kasuwanci da ya kasuwar kasar.

Hakan ya fito ne cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai,Ajuri Ngelale ya raba wa manema labarai.

Shugaban ya bayhana cewa gwamnatinsa na gudanar da shirye shirye masu inganci dan kara karfafa kasuwanci tareda mutanen kasashen ketare.

Yace duk wata matsala da 'yan kasuwar suka fuskanta a baya anyi kokarin maganceta yakuma basu tabbacin yin kasuwanci cikin nutsuwa batare da wani matsala ba.

Tinubu ya kuma tabbatar wa masu zuba hannun jarin na kasashen larabawa cewa indai suka zuba jarinsu zasu samu aminci tare da cikakken hadin kan yan Nijeriya kasancewar kasar na bukatarsu a irin wannan lokaci.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp