Na gamsu da alkiblar gwamnatin Tinubu da Shettima - Buhari


Duk da irin matsalar tattalin arziki da Nijeriya ke ciki da ma matsalar tsadar rayuwa da ake fama da ita a kasar tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ce ya gamsu da alkiblar da shugabannin siyasa na yanzu suka fuskanta.


Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima a garin Daura na jihar Katsina a ranar Asabar.


Tsohon shugaban kasar ya yabawa gwamnatin Bola Tinubu bisa kokarin da take yi na daidaita tattalin arzikin kasar.

Post a Comment

Previous Post Next Post