MTN ya kulle layuka 4.2m da aka kasa hada su da lambar NIN
Kamfanin sadarwa na MTN a Nijeriya ya ce ya katse layukan sadarwa akalla miliyan 4.2 daga cibiyar sadarwarsa yayin da wa'adin da aka kayyade na ranar 28 ga watan Fabrairu na a hada lambobin layuka da shaidar zama dan kasa (NIN) da SIM ya cika.
Kamfanin MTN ya bayyana hakan ne a sakamakon binciken da ya gudanar a ranar Juma’a.
Kamfanin ya ce layukan da aka katse sune na mutanen da suka yi kunnen kashi suka ki hada shi da lambar shaidar zama dan kasa wato NIN.
A cewar kamfanin, tun a cikin watan Disambar 2023 ne hukumar NCC ta ba da umurni ga dukkanin kamfanonin sadarwa a kasar da su tabbatar masu masu amfani da layukan sadarwa su hada layukan wayoyinsu da NIN ɗin su.