Shan miyagun kwayoyi ke sa karuwar rashin tsaro a Nijeriya - Marwa
Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya NDLEA, Buba Marwa, ya ce shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin ‘yan kasar ne ke haddasa rashin tsaro a kasar.
Marwa ya bayyana haka ne a yayin taron wayar da kan mata da matasa a babban birnin tarayya Abuja ranar Juma’a a Abuja.
Ya kuma ce matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin matasa ita ce matsalar kowa wanda a cewarsa ya hada da iyaye da makaranta da sauran jama’a da su kansu matasa.