Majalisar dattijai ta dakatar da Sanata Ningi bisa zargin karkatar da kasafin kudi
Majalisar dattijai ta dakatar da Sanata Abdul Ningi na tsawon watanni uku bisa zargin cusa Naira tiriliyan 3.7 a cikin kasafin kudin 2024.
Ningi shi ne shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da yawan al'umma kuma yana wakiltar Bauchi ta Tsakiya.