Akwai yiyuwar sojojin Nijar su saki Bazoum a Azumin nan
Gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar ta ce a shirye take ta amince da sakin hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum da matarsa Khadija.
Majiyoyi da dama a Nijeriya da makwabciyarta Nijar, sun tabbatar da shirin gwamnatin mulkin soja na sakin hambararren shugaban kasar a cikin ‘yan kwanaki nan na watan Ramadan.
Sai dai an gano cewa babban abin da ke damun manyan jami’an soji a jamhuriyar Nijar shi ne nacewar Bazoum na cewa zai ci gaba da zama a cikin kasar ta Nijar, bisa dalilin cewa ba ya sha’awar komawa wata kasa daban don ci gaba da rayuwa.
Bazoum na samun goyon bayan shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, sannan kuma shugaban Najeriyar kuma jagoran kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS), Bola Tinubu.