Jam'iyyar Labour Party (LP) ta sanar da cewa ta ke
be tikitin takarar shugaban kasa a 2027 ga jagoranta, Peter Obi.
An yanke wannan shawarar ne a babban taron jam’iyyar na kasa da aka gudanar a Nnewi, jihar Anambra, a ranar Laraba.
jam'iyyar ta kuma sanar da sake zaben Julius Abure a matsayin shugabanta tare da wasu shugabannin jam’iyyar bakwai, ciki har da sakataren jam’iyyar na kasa, Umar Faruk Ibrahim.