Gwamnatin Kano ta yi ihsani ga maniyyata aikin hajji kan ƙãri da aka yi.



Gwamnatin jahar Kano ta yi wa maniyyata aikin hajji na jahar rangwamen Naira biliyan 1.453 daga cikin sabon ƙãrin da Hukumar Jigilar Alhazzai ta Najeriya ta yi ga maniyyata aikin hajji na bana.

Da wannan ko Wana maniyyaci a Kano zai samu sauki na Naira 500,000 kenan daga cikin sama da Naira miliyan ɗaya da dubu ɗari tara da hukumar alhazan Najeriyar ta ƙãra a kan sama miliyan huɗu da suka riga suka biya.

Hukumar jigilar Alhazzai ta jahar Kano ta ce wannan rangwame ya shafi waɗanda suka biya kudin aikin hajji ta hannun ta ne kaɗai, kuma sun biya wani abu daga cikin kuɗin, wadda adadin su ya kai maniyyata 2,906 da sukayi rajista da hukumar dan aikin sauke faralin na bana.

Shugaban Hukumar Mahajjatan ta jahar Kano Alhaji Lami Ɗan Baffa a wani taron manema labarai ya ce sunyi wannan ihsani bisa la'akari da yanayin yau, saidai ya ce duk maniyyaci da ke da bukatar zuwa aikin hajjin na bana toh wajibi ya cika sauran Naira miliyan 1.918,032.91 kafin ƙarfe 11:59 na ranar 28 ga watannan na Maris da muke ciki.

Karin kuɗin na aikin hajjin bana ya zo wa wasu maniyyata bagtatan, abin da ya tilasta wa wasun su karɓar kuɗaɗen su da suka bayar tun farko, suka haƙura da zuwa kasa mai tsarki dan sauke faralin saboda babu yadda zasu iya cika wannan ƙãri da aka yi kuma ake buƙatar a biya cikin ƙanƙanin lokaci



.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp