Bashin da ake bin Nijeriya ya doshi Naira Tiriliyan 100 - NBS
Adadin bashin Nijeriya ya karu daga Naira tiriliyan 87.91 (dala biliyan 114.35) a sulusin shekarar 2023 zuwa Naira tiriliyan 97.34 (dala biliyan 108.23) a rubu'in shekarar 2023.
Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana hakan a ranar Talata a cikin rahotonta da ta fitar.
Rahoton ya ce, basussukan da ake bin Nijeriya sun hada da bashin waje da na cikin gida, inda ya karu da kashi 10.73 bisa 100.