Hukumar Anti-Corruption ta Kano ba ta da ikon bincikar Ganduje - Babbar Kotun Tarayya

 


Babbar Kotun Tarayya d ake jihar Kano ta yanke hukuncin cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano da ake wa lakabi da Anti-Corruption ba ta da ikon a bisa doka na binciken tsohon gwamnan jihar kan bidiyon Dala.


Alkali Abdullahi Muhammad Liman shi ne ya sanar da wannan hukunci a Talatar nan wanda ya ce laifin da ake zargin tsohon gwamnan da shi ya fada cikin laifuka da hukumomin gwamnatin Tarayya ke da hurumin bincikarsu. 
Post a Comment

Previous Post Next Post