Buhari ne ya lalata makomar Najeriya - Gwamnan jahar Pilato Caleb Mufwang


Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya zargi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da laifin tabarbarewar tattalin arzikin da ‘yan Najeriya ke fuskanta a halin yanzu.

Gwamnan ya faɗi hakan ne a ranar Litinin a yayin rantsar da masu ba shi shawara na musamman su 22 a gidan gwamnati da ke Jos.

Mutfwang ya ce Buhari ya bar tattalin arzikin kasar cikin mummunan hali ga magajinsa, Bola Tinubu.

Post a Comment

Previous Post Next Post