Gwamnan Katsina Dikko zai ci gaba da ayyukan alherin da za a yi alfahari da APC - Bala Abu Musawa


Alhaji Bala Abu Musawa, mataimakin shugaban jam'iyyar APC a jihar Katsina ya sanar da DCL Hausa cewa Gwamnan jihar Malam Dikko Umaru Radda na ci gaba da assasawa tare da aiwatar da ayyukan alheran da al'ummar jihar Katsina za su ci gaba da alfahari da jam'iyyar APC.

Ci Garin Musawa, Alhaji Bala Abu na magana ne a lokacin da ya jagoranci wani kwamiti na musamman don duba ayyukan da gwamnatin jihar Katsina da shirin inganta ilmin 'ya'ya mata na AGILE da kuma karamar hukuma suke gudanarwa a yankuna daban-daban na jihar.

A wannan karon, kwamitin da ya hada jiga-jigan jam'iyyar APC jami'an gwamnati da 'yan jarida, ya ziyarci kananan hukumomin Malumfashi, Kankara, Musawa da Matazu a shiyyar Funtua ta jihar.

Mataimakin shugaban jam'iyyar ta APC ya ce akwai tsare-tsare da dama da gwamnatin APC ke da su da ke da zummar karade lungu da sako na jihar Katsina domin mutane su samu saukin rayuwa.

Ta fuskar tsaro kuwa, Alhaji Bala Abu Musawa ya ce gwamnatin APC da Malam Dikko Radda ke jagoranta a jihar Katsina, ba za ta gajiya ba wajen ganin ta kakkabe duk wasu masu aikata assha a dazuka da cikin gari domin mutane su koma harkokinsu yadda ya dace.

Ya ce kafa matasan sa kai na 'Community Watch Corp' da Gwamna Radda ya yi, alama ce mai karfi na irin aniyarsa ta kawo karshen matsalar tsaro a lungu da sako na jihar Katsina.

Post a Comment

Previous Post Next Post