UAE ta ɗage haramcin visa kan yan Najeriya


Hadaddiyar Daular Larabawa ta ce za ta dawo da bayar da biza ga 'yan Najeriya, hakan wani mataki ne na karfafa alaka tsakanin kasashen biyu.

Bayanin hakan na a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya fitar a yau Talata.

Wannan dai na zuwa ne shekaru biyu bayan da Daular Larabawa ta sanya wa yan Najeriya takunkumin shiga kasar.

A cewar hukumomin Hadaddiyar Daular Larabawar an dawo da shirin ya fara aiki ne daga ranar 4 ga watan Maris din shekarar 2024, wanda hakan ya samo asali ne sakamakon tattaunawa tsakanin shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da takwaransa na UAE, Sheikh Mohamed bin Zayad Al Nahyan.

Post a Comment

Previous Post Next Post