Dan Madamin Katsina ya ba Labaran Mahmud Yar'adua mukamin Sarkin Fada


Dan Madamin Katsina Hakimin Daddara a masarautar Katsina ya sanar da ba Malam Labaran Mahmud Yar'adua mukamin Fadar Dan Madamin Katsina.

Labaran Mahmud Yar'adua dai ma'aikaci ne a gidan rediyon jihar Katsina a sashen labarai da al'amurran yau da kullum.

A cikin wata sanarwa daga ofishin Dan Madamin Katsina Alhaji Usman Nagogo, ta ce nadin na Malam Labaran ya biyo bayan gano kyawawan halayensa da kuma cancantarsa da wannan mukami.

Hakimin na Daddara da ke cikin karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina ya ce majalisar masarautar Katsina karkashin jagorancin Mai Martaba Sarki Abdulmumin Kabir Usman ce ta lamunce masa ya nada Malam Labaran Mahmud Yar'adua wannan mukami.

Karshe wasikar ta yi addu'a tare da fatan alheri ga wanda aka ba mukamin.

Post a Comment

Previous Post Next Post