Gwamnan Kano ya roki Tinubu da ya bude boda

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya roki shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu da ya bude boda domin a samu wadatar abinci a Nijeriya baki daya. 


Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyarar ban girma da shugaban hukumar kwastam, Adewale Adeniyi, ya kai masa ranar Litinin a Kano.


Gwamna Abba Kabir-Yusuf, ya koka kan mawuyacin halin da 'yan Najeriya ke ciki sakamakon matsi da tattalin arzikin kasar ke ciki, ya ce sake bude iyakokin zai taimaka wajen magance hauhawar farashin kayayyaki da kuma saukar da farashin su.

Post a Comment

Previous Post Next Post