Farashin kayan abinci ya ki sauka duk da rahusar da Dala ta fara yi a Nijeriya


Farashin kayan abinci ya kara kara ta'azzara a makon farko na azumin Ramadana, domin kuwa a makon jiya, masara ta fi sauki a kasuwar Kashere da ke jihar Gombe, inda ake sayar da buhun kan kudi ₦56-57,000, amma a wannan makon kudin buhun masarar ya koma ₦58,000.
 
To a kasuwar Mile 12 International Market Legos ma kudin Buhun Masarar a makon nan ₦68,yayinda a makon daya shude ake saidawa Kan kudi ₦65,000.

Haka nan a kasuwar Gombi da ke jihar Adamawa, masarar ta fi sauki a makon da ya gabata, a makon jiyan dai, an sayar da buhun masarar akan kudi ₦53-55,000, amma a yanzu da ke cikin watan Ramadan kuwa buhun masarar ya koma ₦58,000 har zuwa N60,000.
 
Ko da ya ke a iya cewa Masarar ta yi zarra a kasuwar Mai'adua jihar Katsina, a wannan makon da ke shirin karewa, an sayar da buhun masarar ₦64,000 a kasuwar.

Da alama a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano, kudin buhun masarar bai sauya ba daga na satin da ya shuɗe, domin a wancan makon an sayar da buhun kan kudi ₦58,000, to haka batun yake a wannan satin ma.

Ita ma dai kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna, farashin buhun masarar bai sauya tufafin shi na makon da ya gabata ba, an sayar da masarar kn kuɗi ₦57,000 haka kuwa farashin ya ke a makon da ke shirin yi mana ban kwana.

A bangaren shinkafa kuwa, 'yar gida ta yi tashin gwauron zabi a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano, domin kuwa a makon nan an sayi shinkafar kan kudi ₦130,000, inda aka samu karin ₦10,000 kan na wancan makon da aka saya ₦120,000 cif-cif.
 
A Kasuwar Kashere da ke jihar Gombe kuwa a satin can an sayar da buhun shinkafar Hausar kan kudi Naira ₦115,000-120,000, a makon nan kuwa kuɗin ₦120,000-130,000 ne.

Hakazalika,a kasuwar Mai'adua jihar Katsina ma an sayi buhun tsabar shinkafar Hausa ₦130,000 daidai.

Da muka leka kasuwar Gombi da ke jihar Adamawa kuwa, mun tarar da cewa shinkafar Hausar ta fi sauki a makon da ya shude sama da wannan makon, a gabataccen makon an sayi shinkafar ₦120,000, amma a makon nan an samu karin ₦7,000, inda aka sayar ₦127,000.

Sai dai an samu sauƙin farashin shinkafar gida a kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna da a makon da ya gabata ake sayar da shinkafar gidan ₦130,000, yayin da a satin nan kuwa aka sayar da ita kan kuɗi ₦128,000.

A ɓangaren shinkafar bature kuwa, ta fi tsada a makon da ya shude, inda ake sayar wa kan kuɗi ₦75,000 a kasuwar Gombi da ke jihar Adamawa, amma a makon nan ₦72,000 ne kuɗin buhun shinkafar.

Sai dai batun yasha banban dana Kasuwar Mile 12 International Market Legos,domin kuwa kuɗin Buhun Shinkafar waje ₦83,000 ne saɓanin na baya da ake Sayar wa ₦75,000.

A kasuwar Kashere da ke karamar hukumar Akko a jihar Gombe kuwa, shinkafar waje tafi sauki a makon da ya gabata,an dai sayar da buhun shinkafar ₦80,000 a makon, yayin da a wannan makon kuɗin buhun ya kai ₦82,000-85,000

Shinkafar 'yar waje ta fi tsada a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano a makon nan, ana sayar da buhun shinkafar ₦87,000, yayin da a makon da ya ke karewa kuwa ake sayar da da shi kan kudi ₦85,000.
 
Haka nan an samu sassaucin ₦2000, a kasuwar Giwa ta jihar Kaduna a makon nan, an sayi shinkafar ₦78,000, amma makon da ya shude ₦80,000 ne kuɗin buhun shinkafar baturen.

To bari mu kammala Farashin kayakin abinci na wannan makon da Taliyar Spaghetti, kwalin taliyar ya fi tsada a makon nan da ke shirin karewa a kasuwar Giwa ta jihar Kaduna, ana sayar wa kan kuɗi ₦15,000 dai dai, yayin da a makon da ya wuce aka sayar ₦14500,haka nan batun yake a kasuwar Mile 12 International Market Legos,kudin Kwalin taliyar ₦15000 daidai a wannan makon.

Amma a kasuwar Kashere da ke jihar Gombe kuma kuɗin Spaghetti ya ɗan sauka,inda ake sai da wa ₦13,100, saɓanin na baya da aka sayar ₦13,200.

To a kasuwannin jihohin Katsina ,Kano da Adamawa dai, farashin kwalin taliyar 13,500 ne a makon nan, haka kuma aka sai da a makon da ya shude ma.

DCL HAUSA A'isha Usman Gebi

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp