Nijar ta hana a tsallaka iyakarta, sa'o'i 72 bayan sanar da bude boda kasar da Nijeriya kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito
Har ya zuwa yanzu dai hukumomin Jamhuriyar Nijar din ba su ce uffan ba game da wannan mataki na gwamnatin Nijeriya.
Hukumomin Nijeriya irinsu na Kwastam da na kula da shige da fice na Immigration, sun sassauta hanyoyin shiga da fitar, amma na Jamhuriyar Nijar ba su yi hakan ba.
A ranar 13 ga watan Maris din nan dai ne fadar shugaban Nijeriya ta sanar da bude iyakokin kasa da na sararin samaniya ga Jamhuriyar Nijar tare da janye mata takunkuman da aka kakaba mata tun bayan da aka samu samu juyin mulki da ya yi sanadiyyar hambarar da gwamnatin farar hula ta Bazoum Mohammed.
Category
Labarai
Me su ke bukata da bude boda? Tun kafin yanzu, abinci da sauran kayan masarufin mu na fita ta barayin hanyoyi zuwa Nijar duk da ce wa hukumomin Najeriya sun sa dokar rufewa. Mun rike ma sojan Nijar kan maciji , su na wasa da bindi.
ReplyDelete