Daliban jami'ar Alqalam Katsina sun maka ta kotu

Wasu daliban jami'ar nan mai zaman kanta da ke Katsina, Alqalam University, su uku sun garzaya kotu, inda suke neman da a tilasta wa jami'ar ta tura sunayensu a jerin matasa masu yi wa kasa hidima na NYSC.

Daliban sun je babbar kotun jihar Katsina ne bisa zargin da jami'ar ta yi musu na cewa ba su biya kudin rajistar zangunan karatu hudu ba a jami'ar.

Daliban 'yan gida daya, Hawwa'u Sani Barda, Rabi'atu Sani Barda da Hafsat Sani Barda sun samu takardar shaidar shiga jami'a ta 'admission' a zangon karatu na 2018/2019 da suka kammala a zangon karatu na 2022/2023.

Daliban dai sun yi ikirarin cewa jami'ar ta ki ta tura sunayensu a shirin hidimta wa kasa na NYSC, bisa hujjar jami'ar cewa, daliban ba su biya kudaden rajistar karatu ba.

A lokacin zaman kotun, lauyan masu kara Muhammad Mukhtar Lawal ya ce wadanda ya ke karewa sun zo kotu ne domin neman hakkinsu kamar yadda kundin mulkin kasa na 1999 ya tanadar.

Mukhtar Lawal ya ce takardar ta nemi izinin kotu domin a duba wannan shari’a.

Bayan gabatar da karar, Alkalin kotun, Mai shari’a Abbas Bawale, ya ce ya kamata masu karar su shigar da bukatar kotu ta aike sammace ga jami'ar domin lauyoyinta suma su halarci zaman shari'ar.

Sai dai Mai Shari'a Abbas Bawale ya ba masu karar damar yin nazari sosai a kan wannan karar, inda aka basu wa'adun kara shigar da karar wadda ta hada da bukatar kotu ta aikawa jami'ar takardar sammace.

Ya ce bayan haka za a bi hanyoyin da suka dace don isar da sammacen, daga nan kuma kotu ta sanya ranar da za'a fara shari'ar.

4 Comments

  1. Allah yasa mudace

    ReplyDelete
  2. Akwai wani azzalumi a makarantar mai cutar dalibai da fakewa da sunan zai taimaka musu. Shiyake karbar kudin registration a hannun irin wadannan daliban ba tareda sanin hukumar makarantar ba. Haka ya faru da kanina, sai da yakai year 4 sukace baya makarantar. Basu sanda shiba. Kuma wannan azzalumin ma’aikacin makarantar yana bashi sakamakon jarabawar ko wace semester bayan sunyi jarabawa ya kawowa iyayen shi. In shaa Allah Asirin shi zai tonu bana.

    ReplyDelete
  3. Lazy students with careless parents,meyasa students bazasu biyawa kansu kudin makaranta da ka su bah,are they computer illiterate?? Sanda nake school din,I pay my fees and hostel fees myself in front of my dad yasa bank details dinsa ya biya,he prints the slip himself for me.Duk sanya be nan I do it on my own in naje schoool inyi printing slip nabi process na karban receipt.and I do it as early as possible.why will you give someone else ur fees to pay for you for crying out loud????

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp