Nijeriya za ta bude cibiyar rubuta jarabawar NECO a kasar Saudiyya

Hukumomi a Nijeriya sun sanar cewa ba da jimawa ba za a bude sabuwar cibiyar da za a rika zauna jarabawar karshe ta 'yan sakandare ta NECO a kasar Saudiyya.

Hakan kuwa ya biyo kammala tantance cibiyar zauna jarabawar da ke makarantar Nigeria International School, Jedda kasar Saudi Arabia da karamin ministan ilmi Dr Yusuf Tanko Sununu ya jagoranci tawaga ta musamman don gudanar da wannan aiki. Daga cikin tawagar akwai Magatakardar hukumar shirya jarabawar ta NECO na Nijeriya Prof Ibrahim Wushishi.

A lokacin ziyarar, tawagar ta samu damar ganawa da hukumomin makarantar da duba duk abubuwan da suka kamata a mallaka kafin a bude cibiyar zauna jarabawar.

Post a Comment

Previous Post Next Post