Dala na ci gaba da sauka, farashin kayan abinci ma na ci gaba da sauka a sassan Nijeriya

Dala na kara sauka, farashin kayan abinci na kara sauka a wasu kasuwannin Nijeriya.


A makon nan dai an sayi buhun masara a
kasuwar Mile 12 International Market dake Lagos an sayi buhun masara kan kuɗi ₦63,000, amma a makon da ya kare kuɗin buhun ₦65,000 ne, hakan na nuni da cewa an samu canjin ₦2000 kenan a kasuwar.

A kasuwar Mai'adua jihar Katsina ma an ɗan samu saukin ₦2000 kan kudin buhun Masara a wannan makon da muke shirin fita, inda aka sayi buhun kan kudi ₦62,0000 a satin nan, sai dai a makon da ya gabata kuwa ₦64,000 kuɗin kowane buhu na masara.

A makon da ya wuce an sayi buhun Masara ₦57,000 a kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna, hakan kuwa aka sai da a makon nan.

Sai dai, an sayar da buhun Masara ₦58,000 a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano a wannan makon, yayin da a wancan satin kuma aka saya ₦57,000,an samu karin dubu guda kenan kan farashin makon da ya shude.

Ita kuwa kasuwar Kashere da ke jihar Gombe, farashin buhun masara a wannan makon ya tashi sosai, a wancan makon dai an sayi buhun ₦52-53,000, amma a makon nan ₦60,000 daidai ne kuɗin buhun masarar.

Idan muka leka a kasuwar Gombi da ke jihar Adamawa kuwa, farashin bai sauya ba, an sayi buhun ₦59-60,000, haka nan zancen ya ke a makon nan da ke yi mana ban kwana ma.

Har ila yau, shinkafar Hausa ta fi tsada a kasuwar Karamar Hukumar Gerie da ke jihar Adamawa, a wannan makon, an sayi buhun shinkafar ₦143,000, amma a makon jiya kuma ₦139,000 kuɗin buhun yake, an samu karin ₦4,000 kenan a tsakanin kwanaki 7.

Amma farashin shinkafar bai canza zani ba a kasuwar Kashere da ke karamar hukumar Akko a jihar Gombe, a makon da ya shude, ana sai da buhun ₦108-110- haka nan akwai na ₦115-120,000 ya dai danganta da kyan shinkafar, haka nan aka saya a wannan satin.

Da muka leka kasuwar Giwa ta jihar Kaduna kuwa, mun tarar da cewa kudin buhun shinkafar yana kamar yadda yake a satin can, an saya ₦128,000 satin da ya gabata, haka batun ya ke a satin nan ma .

Sai dai fa farashin shinkafar na ci gaba da sauka a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano sakamakon saukar Dala da CFA, an sayar da buhun shinkafar ₦120,000 a makon da ya gabata, yayin da a yanzu kuwa ake sai da ta ₦110,000 cif, an samu sassaucin ₦10,000 a makon nan.

A daidai lokacin da aka samu sauƙin ₦10,000 a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano, ita kuwa kasuwar Mai'adua jihar Katsina kuɗin buhun ya fi na makon da ya shude tsada, inda a wancan aka sayi buhun ₦125,000, sai dai a makon nan ₦130,000 ne kuɗin buhun yake a kasuwar.

A kasuwar Mile 12 International Market da ke Lagos kuɗin buhun shinkafar ₦120,000 a wannan makon da ke dab da kare wa.

Kuɗin buhun shinkafar waje kuma ₦75,000 a kasuwar Mile 12 International Market dake Legos, sai dai shinkafar ta fi sauki a wasu kasuwannin Arewacin kasar, inda aka sayi buhun shinkafar ₦65,000 a kasuwar Mai'adua jihar Katsina wannan makon.

Ita ma kasuwar Dawanau da ke jihar Kano kuɗin buhun shinkafar baturen ya faɗi, a makon da ya shude an sai da buhun ₦83,000, yayin da a makon nan aka sayar kan kuɗi ₦75,000.

Hakan a kasuwar Kashere da ke jihar Gombe ma kudin buhun shinkafar bature ya sauka sosai, an sayi buhun ₦75,000 makon nan, yayin da wancan makon kuwa aka sayar ₦80,000 daidai.

Sai dai a Kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa kuwa, farashin shinkafar bature ya sake tashi a wannan makon, inda aka sai da buhun ₦78,000 a satin nan, amma a makon da ya kare kuma ₦72,000 kudin buhun shinkafar, an samu karin kimanin ₦6,000 kenan.

An sayi shinkafar waje ₦78,000 a kasuwar Giwa dake jihar Kaduna a makon jiya, yayin da a wannan makon kuwa aka sai da kan kudi ₦75,000.

To bari mu ƙarƙare farashin kayan abincin na wannan makon da Taliyar Spaghetti.

To wannan makon ma farashin taliyar ya ɗan sauka a kasuwar Mile 12 International Market Lagos, an sayi 
Kwalin taliyar kan kudi ₦14,000 a makon nan, sai dai a makon can ₦15,000 ne daidai kuɗin Kwalin taliyar.

Amma kasuwar Giwa dake jihar Kaduna kuwa kuɗin Kwalin taliya ₦14,500 ne a makon nan,₦14,500 ɗin aka saya makon da ya shude.

A kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa, kudin Kwalin taliyar bai sauya ba daga na makon da ya gabata, an sayi kwalin kan kudi ₦13,200 a wancan makon, haka nan a satin nan ma.

Sai dai fa kasuwar Kashere na jihar Gombe Kwalin taliyar ya fi na makon da ya shude tsada, an sayi kwalin ₦13,000, amma a makon nan kuɗin Kwalin ₦13,200 ne.

A kasuwar Dawanau na jihar Kano ana sai da Kwalin taliya ₦13,500 a makon nan, haka nan a wannan makon ma.

Kwalin taliyar ya fi tsada a makon nan a kasuwar Mai'adua jihar Katsina, an sayi Kwalin ₦13,000 a makon da ya kare, yayin da a wannan makon dake dab da karewa aka sai da ta kan kuɗi ₦13,500

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp