An samu Gidauniyar da ta yi karo-karon kudi sama da Naira Milyan 140 don tallafa wa gajiyayyu cikin watan Ramadan a Kano

Gidauniyar Peace Ambassadors Association, ta tattara kudi daga cikin mambobinta da suka haura Naira milyan 140 don su sayi kayan abinci, sutura da kudi tsaba da za su rarraba ga mabukata masu karamin karfi a jihohin arewacin Nijeriya.

Daya daga cikin mambobin kungiyar Amb Usman Muhammad Maliya ya ce sun sayi madara katan 300 da 
Indomie katan 300 da kuma buhunan shinkafa 300.

Sauran kayan da suka saya don rarrabawa su ne taliya katan 300 da 
Macaroni katan 300.

Sannan Amb Usman Muhammd Maliya ya ce sun sayi shaddoji da yadukan da za su raba wa iyalan mabukata da kuma kudi tsaba da duk za su rarraba don saukaka rayuwa musamman duba da halin da ake ciki.

Post a Comment

Previous Post Next Post