Jam'iyyar PDP na son a yi bincike kan zargin cushen N3.7trn a kasafin 2024


 Jam'iyyar PDP na son a yi bincike kan zargin cushen N3.7trn a kasafin 2024


Jam'iyyar adawa ta PDP a Nijeriya ta bukaci a gudanar da bincike kan zargin cushen kudi N3.7trn a kasafin kudin 2024.Jam'iyyar ta PDP ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da sakataren yada labaranta na kasa, Debo Ologunagba ya fitar a Abuja.


Ologunagba ya ce binciken zai taimaka wajen gano abubuwan da suka sa aka dakatar da Sen.  Sanata Abdul Ningi (PDP-Bauchi) da Majalisar Dattawa ta yi, yana mai cewa an dakatar da Ningi ne ba tare da yin cikakken bincike kan kasafin kudin da ake zargin sa ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post