Zan je da kaina in sanar da shugaba Tinubu halin matsin rayuwa da ake ciki - Gwamna Abba


Gwamnan jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf ya ce shi da kashin kansa zai sanar da shugaba Tinubu halin da talakawan Nijeriya ke ciki na matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a lokacin da yake ganawa da 'yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki a Kano.

Ya koka kan yadda a kullum rana ake samun tashin farashin kayayyaki, inda ya ce hakan na bukatar daukin gaggawa don a yi wa tufkar hanci.

Gwamna Abba Gida-Gida ya ce gwamnatin jihar Kano za ta yi duk abin da ya dace son samar da yanayi mai kyau ga 'yan kasuwa don bunkasar tattalin arziki.

Post a Comment

Previous Post Next Post