Uwargidan shugaban Nijeriya Sanata Oluremi Tinubu ta ba 'yan kasar tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za su fita daga cikin halin kuncin da suka shiga.
Oluremi Tinubu ta ba da wannan tabbacin a lokacin da take ganawa da matan gwamnonin kasar a Abuja.
Ta ce shekarar 2024 cike take da zaman lafiya, ci gaba da sauran abubuwan ci gaba da 'yan kasar za su mora.