Zaman lafiya ya dawo a kananan hukumomi 13 na jihar Katsina - GwamnatiDikko Umar Raɗɗa
 

Mataimakin Gwamnan jihar Katsina Alhaji Faruq Lawan Jobe, ya ce gwamnatin jiha ta yi kokari ta maido da zaman lafiya a kananan hukumomi 13 cikin 22 da ke fama da matsalar tsaro a jihar.

Jaridar This day ta rawaito cewa Faruq Jobe na magana ne a gaban 'yan jarida, inda ya ce an samu wannan nasarar ne ta dalilin ayyukan jami'an sa kai na 'Community Watch Corp' da gwamnatin ta kirkiro, hadin guiwa da sauran jami'an tsaro a jihar.

Daga cikin kananan hukumomin da tsaron ya fara inganta, a ta bakin mataimakin Gwamnan jihar, akwai Batagarawa, Dutsinma, Bindawa, Kusada, Funtua, Danja, Bakori, Malumfashi, Kafur, Musawa, Ingawa, Charanci da Matazu.

Post a Comment

Previous Post Next Post