Za mu tabbatar da samar da ilmi mai inganci a jihar Zamfara - Gwamna Dauda

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawan Dare ya sake nanata kudirin gwamnatinsa na tabbatar da cewa yaran da ke tasowa sun samu ilmi mai inganci a jihar.

Gwamnan na magana ne a wajen gasar wasanni ta shekarar 2024 karo na uku da aka gudanar a makarantar Almufida International Academy, Gusau.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan jihar, Malam Sulaiman Bala Idris ya aike wa DCL Hausa, ta ce wannan makaranta, har ta karrama Gwamna Dauda da lambar girmamawa ta GCFC.

Sanarwar ta ce Gwamnan ya nuna jin dadi da farinciki sosai na yadda ya ga daliban makarantar na fahimtar karatu da kuma zalaka a wasannin da aka gudanar a cikin gasar.

A jawabinsa a wajen taron, Gwamnan ya yaba wa hukumar gudanarwar makarantar da ta ke kokarin tsare ka'ida da bin dokoki da ka'idojin da aka gindaya don ilmi ya inganta a jihar.


Post a Comment

Previous Post Next Post