Mutane 7 sun mutu a sakamakon
turmutustu wajen siyan buhun shinkafar da hukumar kwastam ta ke sayarwa a jihar
Legas.
Bayanai sun ce dubban mutanen ne suka fita da nufin
sayan shinkafar, yayin da ake kafa layi tun karfe uku na dare don sayan
shinkafar a ofishin hukumar da ke unguwar Yaba, kan naira dubu 10 akan Kg 25 na
shinkafar.
Wannan ya biyo bayan shelar da hukumar kwastom
din ta yi na fara sayarwa da ‘yan kasa shinkafar da ta kama hannun masu fasakwauri,
sai dai wani abu mai daure kai shine yadda hukumar tayi ikirarin cewa shinkafar
na da illa ga lafiyar jama’a, sai gashi tana sayarwa.
Rahotanni sun ce cikowar mutane ta haddasa
turmutsutsu yayin da aka tattake wasu mutane 7 har suka cimma ajalin su, cikin
su kuwa har da mace mai tsohon ciki.
Wasu bayanai sun ce turmutsutsun ya faru ne
lokacin da yan daba suka yi yunkurin shiga ofishin hukumar da karfin tsiya.
Wasu daga cikin wadanda suka zanta da manema
labarai sun ce jamia’n na custom sun yi iya bakin kokarin su wajen shawo kan
matsalar amma ‘yan dabar sun fi karfin su kasancewar basu shiryawa faruwar
hakan, ba dalilin da ya sanya ‘yan dabar suka fi karfin su.
Bayanai sun ce jami’an ‘yan sanda sun je wajen
sai dai sun je ne ba don shawo kan matsalar ba, illa dai don samun nasu buhun
shinkafar.