Hukumar hana cin
hanci da rashawa ta EFCC ta sanar da kwato naira biliyan 60 cikin kasa da
kwanaki dari, yayin da ta karbi korafe-korafen cin hanci guda dubu 5.
Yayin da yake
jawabin ayyukan da yayi cikin kwanaki 100 da zaman sa shugaban hukumar Mr Ola Olukoyede
ya ce cikin korafe-korafe dubu 5 din da aka shigar gaban hukumar ta amince a
fara bincike kan sama da dubu 3.
Ya ce bayan naira
biliyan 60 din an kuma kwato wata dala miliyan 10 cikin kasa a watanni 4 da yayi
a ofis.
Mr Ola ya ce lamarin
cin hanci da rashawa abu ne da ke bukatar hadin kan jama’ar kasar kasancewar EFCC
ba zata iya ita kadai.
Baya ga wannan
jamawabi, shugaban na EFCC yayi korafi game da karancin ma’aikata, yana mai
cewa hukumar da ke sanya idanu kan mutane sama da miliyan 150, tana da ma’aikata
4,800 don haka ba za’a ga tasirin aikin da suke yi ba.
To ai a banza don an kwace a hanun wani, don nasan kuma zasu koma a aljihun wani, don haka ina kira da EFCC da su kawo kudin na aje su a wajena
ReplyDelete