Gwamnatin tarayya ta
sake gargadin kungiyoyin kwadago a Najeriya kan shirin zanga-zanga da suke yi a
cikin makon nan.
Wannan na zuwa ne bayan
da wasu kungiyin fararen hula 65 suka nuna goyon bayan su ga kungiyoyin
kwadagon da kuma tabbatar musu da bada goyon baya a ranar zanga-zangar.
A karshen makon jiya
ne shugaban kungiyar NLC Joe Ajero ya zargi gwamnatin tarayya da shirya ‘yan
dabar da zasu kai musu hari a ranar zanga-zangar, zargin da gwamnati ta
musanta.
Da yake jawabi
babban mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Mr Bayo Onanuga
ya ce tuni ‘yan sanda suka mikawa kungiyoyin daya bayan daya takardun gargadin
fita zanga-zangar don haka abu mafi a’ala shine su janye kudurin nasu.
Sai dai kuma duk da wannan gargadi da gwamnatin tarayya ta sabunta,
kungiyar ta NLC ta ce babu gudu ba ja da baya wajen gudanar da zanga-zangar gobe
Talata da kuma jjibi Laraba.