Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya ya kai ziyarar jajantawa da ta'aziyya ga al'ummar kauyen Yarnasarawa a cikin karamar hukumar Faskari ta jihar bayan da harin da 'yan ta'adda suka kai wa kauyen a makon jiya.
Harin 'yan bindigar dai ya yi sanadiyyar mutuwar mutune 8 kamar yadda sanarwar da daraktan yada labaran ofishin Sakataren Gwamnatin jihar Abdullahi Aliyu Yar'adua ya aike wa DCL Hausa.
Sanarwar ta ce 'yan bindigar sun farmaki kauyen, inda suka kuma sace mutane 45 da suka hada da mata 37 da maza 8 da mafiyawansu yara ne.
Gwamnan jihar ta Katsina da ya samu wakilcin Sakataren Gwamnatin jihar Abdullahi Garba Faskari, ya nuna jimami, alhini da takaicin abin da ya faru a wannan kauye, inda ya yi ta'aziyya tare da addu'ar Allah Ya gafarta wa wadanda suka rasu.
Gwamnan wanda ya jaddada kudurinsa na ci gaba da yaki da ta'addanci har sai an kawo karshen ayyukan 'yan ta'adda a jihar, ya kuma bi gida-gida inda ya yi ta'aziyyar wadanda suka rasu.
Sannan Gwamnan ya kuma ziyarci motoci 8 da 'yan ta'addar suka kona da gidaje 10 da su ma aka kona.