Muna rokon Allah Ya yaye mana matsalar tsaro a jihar Katsina - Bala Abu Musawa


Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na jihar Katsina Alhaji Bala Abu Musawa, ya ce a halin da ake ciki matsalar tsaro ce kadai ce ke ci wa al'ummar jihar tuwo a kwarya, inda ya ce ana ci gaba da addu'o'i na neman zaman lafiya dawwamamme a lungu da sako na jihar.

Alhaji Bala Abu Musawa na magana ne, a Dutsinma a lokacin wata ziyarar gani da ido ta duba wasu ayyuka da ganawa da shugabannin jam'iyyar APC a matakin karamar hukuma da mazabu.

Jam'iyyar APC a jihar Katsina dai ta fara wannan ziyarar ne a makon jiya da shiyyar Daura mai kananan hukumomi 12, inda a wannan makon ta fara a shiyyar Katsina da ke da kananan hukumomi 11, da aka fara da kananan hukumomin Danmusa, Safana, Dutsinma da Kurfi.

Jigon jam'iyyar ta APC a jihar Katsina ya ce addu'a kasancewarta takobin mumini, ita ce kadai ya kamata al'ummar jihar Katsina ta kara yi domin a kawo karshen matsalar ta tsaro da ta ke addabar wasu yankunan jihar.

Duk da Alhaji Bala Abu Musawa ya ce ana samun sauki a matsalar tsaro a halin yanzu, amma dai ya nanata kudirin gwamnatin Dikko Umaru Radda a karkashin jam'iyyar APC cewa a duk rana a tsaye take don ganin ta kakkabe ayyukan ta'addanci a jihar.

Ya nusar da mutane cewa wannan matsala ta tsaro ba rana daya ta shigo ba, sai a hankali za ta kwaranye, don haka, ake bukatar mutane su rika ba da hadin kai musamman ga jami'an tsaro don su inganta aikinsu na samar da tsaro.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp