Dalilin da yasa muka cire tallafin man fetur – Tinubu.

 Dalilin da yasa muka cire tallafin man fetur – Tinubu.


 Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya ce matakin cire tallafin man fetur abu ne mai kalubale, amma matakin da ya dace tare da bunkasa harkokin makamashi da kuma bunkasa tattalin arzikin kasar.


Shugaban ya bayyana haka ne a yayin bude taron kasa da kasa kan makamashi na Nijeriya (NIES 2024) karo na 7 a dakin taro na Banquet Hall dake Aso Villa, Abuja.


Tinubu ya ce domin rage tasirin cire tallafin man fetur na kankanin lokaci ga marasa galihu, gwamnatinsa ta himmatu wajen aiwatar da Shirye-Shirye daban daban. 


Tinubu, wanda ya samu wakilcin ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Alhaji Mohammed Malagi, ya ce tallafin man fetur a tsawon shekaru ya kawo cikas ga albarkatun tattalin arzikin Nijeriya.


Don haka gwamnati na iya kokarinta wajen farfado da tattalin arzikin Nijeriya Amma wannan ba karamin aiki bane da gwamnatin ta dauko, saboda haka aka fito da wayannan  tsare tsare. 


Yace kudaden da aka ware a baya don tallafawa albarkatun man fetur yanzu an karkatar da su zuwa bunkasa da inganta makamashinmu da sauran ababen more rayuwa a kasar. 

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp