Majalisar Nijeriya nason gwamnatin kasar ta bullo da tsarin da zai sauke farashin kayan abinci a kasar.

 Majalisar dattawan Nijeriya ta bukaci gwamnatin tarayyar kasar da ta bullo da wani shiri na rage kudin abinci a matsayin wani mataki na wucin gadi domin dakile illar yunwa da karancin abinci a kasar.


Majalisar ta kuma yi kira ga ma’aikatar noma da samar da abinci ta kasar da ta yi hulda da sauran masu ruwa da tsaki, domin lalubo hanyoyin da za'a magance tsadar abinci a fadin kasar.


Gabatar da shirin yazama dole, domin akwai bukatar abullo da sabbin dabaru domin da zasu farfado da matsalar abinci da ake fuskanta. 


Wadannan kudurori sun biyo bayan kudirin da babban mai shigar da kara na majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume daga ( Borno ta Kudu), da kuma Sanata Saliu Mustapha daga( Kwara ta tsakiya) da wasu da yawa daga cikinsu suka amince da wayannan kudurorin a yayin zaman majalisar.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp