Za a hukunta 'Yansandan da ke amfani da sunan IGP wajen aikata ba daidai ba.

 Za a hukunta 'Yansandan da ke amfani da  sunan IGP wajen aikata ba daidai ba. 



Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya, IGP Kayode Adeolu Egbetokun ya yi kakkausar suka ga duk wani nau’i na karbar kudi tare da yin gargadi ga duk wani jami’in da ya yi amfani da su ko kuma a sakaya sunansa wajen aikata miyagun ayyuka.



Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa Sufeto Janar din ya nuna matukar damuwarsa, inda ya jaddada cewa irin wannan aika-aikar na zubar da mutuncin sa da kuma rundunar ‘yan sandan Nijeriya, wanda hakan ke zubar da mutuncin jama’a.


Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar a ranar Laraba.



IGP din ya jaddada cewa duk wani jami’in da aka samu da laifin yin amfani da sunansa da laifin zamba ko karbar kudi zai fuskanci hukunci mai tsanani. Daga nan sai ya bukaci jami’an da su tabbatar da gaskiya da sanin ya kamata, yana mai jaddada cewa mutuncin rundunar ‘yan sandan Nijeriya na cikin hadari idan ba a duba irin wannan ba, ‘’in ji sanarwar.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp