Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na jihar Katsina Alhaji Bala Abu Musawa ya sanar cewa gwamnatin Malam Dikko Umaru Radda a jihar ta dora harsashin gina jihar mai kwari da za a mora shekara da shekaru.
Alhaji Bala Abu Musawa na magana ne a lokacin da ya jagoranci wata tawaga ta musamman domin duba wasu ayyuka da aka assasa a kananan hukumomin Sandamu, Baure, Zango da Mai'adua a shiyyar Daura jihar Katsina.
Ya ce ire-iren tsare-tsaren ayyukan ci gaban da gwamnatin APC a jihar Katsina ta zo da su, za su sauya rayuwar mutanen jihar da kara inganta musu rayuwa.
Mataimakin shugaban jam'iyyar APC din, wanda shi ne Ci Garin Musawa, ya ba da tabbacin cewa, a gwamnatin nan da Malam Dikko Umaru Radda ke jagoranta, jihar Katsina za ta zamo a sahun gaba wajen ci gaba ba ma a Nijeriya ba, har ma a idon duniya.
A duk kananan hukumomin da aka ziyarta, tawagar ta samu duba wasu ayyuka a lunguna da sako na wadannan kananan hukumomi domin tabbatar da ingancin aiki da kara karfafa guiwa ga 'yan kwangilar da ke gudanar da wadannan ayyuka, na su kammala cikin lokacin da aka kayyade musu.
Daga cikin tawagar akwai Hon Ya'u Umar Gwajo-gwajo, mai ba Gwamna shawara ta musamman kan harkokin siyasa da Hon Shafi'u Abdu Duwan da Hon Shehu Kabir Jani da Alhaji Sabo Musa Hassan da Mamman Yaro Batsari da sauran jiga-jigan jam'iyyar APC ta jihar Katsina.