Hukumar kwastam ta bayyana shirinta na raba kayan abinci ga yan NajeriyaDangane da halin kunci da ake fama dashi a Najeriya, hukumar kwastam ta bayyana shirin ta na raba kayan abinci da da hukumar ta kama ga ‘yan Najeriya.

Shugaban Hukumar Bashir Adewale Adeniyi, ya ce za a raba kayan abincin ne bayan an tantance mutane.

Hakan dai na a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Abdullahi Maiwada ya fitar a yau Talata, Adeniyi ya jaddada aniyarsa na shirin samar da abinci kamar yadda shugaba Bola Tinubu ya ƙudiri aniya.

Post a Comment

Previous Post Next Post