Ma'aikatan Jihar Neja sunfara yajin aikin sai Baba tagani.

 Ma'aikatan Jihar Neja sunfara yajin aikin sai Baba tagani. 

Kungiyar kwadago a jihar Neja ta sanar da daukar matakin fara yajin aiki na masana'antu wanda zai fara aiki daga ranar Laraba 21 ga Fabrairu, 2024.


 A cikin wata wasika da ta aikewa gwamnatin jihar Neja ta ofishin sakataren gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar shugaban kungiyar NLC na jihar Idris A. Lafene da shugaban kungiyar TUC na jihar Ibrahim Gana.

 matakin zai cigaba har sai gwamnati ta warware duk wata takaddamar da ke tsakaninta da kungiyar kwadago ta jihar.


Kungiyar kwadagon ta bukaci gwamnatin jihar da ta sauya duk wasu nade-naden siyasa a matsayin manyan daraktocin kudi, ayyuka da gudanarwa na  hukumomi.


Haka kuma ta bukaci gwamnati da ta sauya nadin shugabanni da mambobi da kwamishinonin dindindin na hukumar ma'aikatar kananan hukumomi da na hukumar da kuma nadin manyan daraktoci na wasu hukumomi.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp